Kaso 63 na matan dake karatu a jami’o’in Nigeria sun fuskanci cin zarafin lalata—RAHOTO

0
29

An jima ana yin zargin cewa mafi yawa daga cikin yan mata da matan aure na fuskantar cin zarafin lalata musu rayuwa, a lokacin da suke yin karatu a wasu daga cikin jami’o’in Nigeria, zargin da a mafi yawancin lokuta wasu malaman ke karyatawa, yayin da wasu ke tabbatar da aikata mummunar dabi’ar.

Karanta karin wasu labaran:::Sojojin jamhuriyar Niger sun kashe mayakan Lakurawa

Wasu bayanai da suka fito a baya-bayan nan sun nuna cewa kaso 63, cikin dari na matan dake yin karatu a jami’ar Bayero ta Kano da sauran jami’o’in Nigeria sun fuskanci cin zarafi a lokacin karatu, kamar yadda matan suka tabbatar da kan su.

Daliban sun zayyano abubuwan da suke fuskanta game da cin zarafin, lokacin da suke amsa tambayoyin da masu binciken suka yi wa dalibai mata 3,528 a jami’o’in game kan cin zarafi ta hanyar lalata.

Wannan ya nuna cewa a cikin dukkan dalibai mata 10 dake karatu a jami’a 6, daga cikin su sun taba fuskantar cin zarafin lalata dasu.

Jaridar Aminiya, ta rawaito cewa, wani binciken cin zarafin dalibai da kungiyoyin Alliance for Africa (AFA) da kuma Kwamitin Daraktocin Jinsi na Jami’o’in Nijeriya (CGDNU) suka gudanar ya bayyana cewa daliban da suka fuskaci cin zarafi ta hanyar lalatar sun fito daga wasu jami’o’i 12 a yankunan Arewa da Kudancin Nijeriya.

Rahoton yace duk da binciken nasu har yanzu akwai matan da aka lalata a jim’o’i amman ba za’a taba sani ba saboda suna jin tsoron bayyana abin daya faru dasu, saboda gudun abinda kaje yazo.

  • Jami’o’in su hada da Jami’ar Bayero ta Kano da Jami’ar Jihar Kaduna da Jami’ar Abuja da Jami’ar Jihar Nasarawa da Jami’ar Jos  da Jami’ar Ibadan da Kuma Jami’ar Legas.
  • Sauran su ne Jami’ar Jami’ar Ibadan da Jami’ar Fatakwal da Jami’ar Jihar Delta da Jami’ar Fasaha ta Tarayya ta Owerri da Jami’ar Jihar Imo da Jami’ar Chukwueneka Odumegwu Ojukwu da ke Jihar  Anambra.
  • Babbar Darakatar AFA, Iheoma Obibi, a yayin gabatar da sakamakon binciken ta ce, a yayin da ake tsammanin jami’o’in Nijeriya su zama cibiyoyin kare ilimi da samar da Æ™wararrun, abubuwan da binciken ya gano ya nuna irin munanan abubuwan da dalibai mata ke fuskanta a yayin karatun jami’a, ba tare da an dauki wani kwakkwaran matakin yi wa tufkar hanci ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here