Hukumar kididdiga ta Nigeria (NBS) tace yanayin rashin aikin yi a tsakanin matasan kasar ya karu inda yakai 4.3, cikin a cikin sashi na biyu na shekarar 2024.
Hukumar tace rashin aikin yi a tsakanin matasa ya ragu daga 8.4 cikin kashin farko zuwa 6.5 a kashi na biyu na 2024, yayin da rashin aikin yi a tsakanin maza yake a kashi 3.4, sai mata masu kashi 5.1.
Karanta karin wasu labaran:::Kaso 63 na matan dake karatu a jami’o’in Nigeria sun fuskanci cin zarafin lalata—RAHOTO
A birane, rashin aikin yi ya kai kashi 5.2, yayin da a karkara ya kasance kashi 2.8.
NBS tace yawan ma’aikatan da ke cikin jama’ar da suka kai shekarun aiki ya kasance kashi 76.1 cikin kashi na biyu na 2024.
Adadin ya nuna yadda aka samu ƙarin kaso 73.1 a kashin farko na 2024, amma duk da haka, wannan adadin ya ragu idan aka kwatanta da kaso 77.1 da aka samu a kashi na biyu na 2023.
Hakazalika, adadin ’yan Najeriya da ke aiki ya ragu zuwa 9.2 a kashi na biyu na shekarar 2024, idan aka kwatanta da kashi 10.6 a kashin farko na wannan shekara.