Fadar shugaban Nigeria Bola Tinubu, ta mika kokon babar ta ga mambobin majalisar dokokin kasar akan su amincewa bukatar ta ta neman sahalewa kudirin dokar sauya fasalin haraji wadda shugaban ya aikewa majalisun duk da irin Cece kucen da ake yiwa kudirin.
Rahotanni sun nuna cewa fadar shugaban ta matsu akan yan majalisar su amincewa kudirin don fara aiki da dokar a ranar 1 ga watan Junairu na shekarar 2025.
Tunda farko wani kwamitin fadar shugaban kasa akan karbar haraji ne ya bayar da shawarar sauya daukacin yanayin karbar haraji da Kuma rabon sa, inda ake kyautata zaton a wasu fannin kudirin ana son tauye yankin arewacin Nigeria.
Gwamnonin Arewa da masu rike da sarautar gargajiya na yankin sun yi fatali da kudirin, inda suka nemi kar yan majalisar yankin su amincewa kudirin, saboda an bawa shugaban kasa shawarar jingine kudirin yaki, tare da shan alwashin tabbatar da shi.
A yau litinin ana sa ran majalisar dokokin Nigeria zata zauna da yan kwamitin harajin don tattaunawa akai.
Kudirin dokar shine zai sanya a kara harajin VAT na siyan kayayyaki, da kuma fifita wasu jihohin Nigeria a wajen rabon harajin da aka tattara.