Mai rikon mukamin Hafsan sojojin kasa, na Nigeria Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya nemi a karawa sojoji wani kaso a cikin kasafin kudin shekara-shekara musamman 2025, don samar da gidaje ga dakarun sojin, wanda hakan zai kara inganta walwala da jin dadin jami’an.
:Kananun yara fiye da dudu 150 sun kamu da cutar HIV a Nigeria
Oluyede, ya bayyana hakan lokacin da kwamitin majalisar dattawa mai kula da harkokin soji ya kai musu ziyarar ta’aziyyar mutuwar tsohon hafsan sojojin kasa Taoreed Lagbaja, yana mai cewa a kowacce shekara ana daukar sabbin sojoji da yawan su yakai dubu sha biyar ba tare da yin la’akari da cewa suna bukatar wajen zama ba, kuma sabbin dakarun basu fiya samun wadataccen wajen da zasu yi rayuwa ba, saboda karancin gidajen da rundunar sojin ke fuskanta.
Mukaddashin hafsan sojin yace matsalar karancin gidajen zata kara ta’azzara da zarar an samu zaman lafiya a Nigeria wanda daga wannan lokacin dole ne sojojin dake filin daga su koma bariki don cigaba da rayuwa.
Ya yi kira ga Majalisar Dattawa da ta tallafa wa rundunar wajen magance wadannan matsaloli a kasafin kudin shekara mai zuwa don inganta tsaro a kasa.