Hukumar karbar koke-koke da hana cin hanci da rashawa ta jihar Kano (PCACC) ta gano yadda wasu masu son zuciya suka sace buhun shinkafar tallafi 16,800 , tare da sauya mata mazubi don siyarwa.
:::Yahaya Bello ya musanta zargin kwashe naira biliyan 110 na jihar Kogi
Hukumar ta bankado shinkafar ce a wani wajen adana kayayyaki mallakin wani mutum da ba’a bayyana sunan sa ba.
Shugaban hukumar Muhyi Magaji Rimin Gado, ne ya sanar da hakan a ranar Talata lokacin da yake zantawa da manema labarai, inda yace wasu masu kishin kasa ne suka sanar da hukumar wannan abu har aka kai ga samun nasarar gano inda aka boye shinkafar, wadda aka bayyana cewa an samar da ita don shirin ciyar da mutane abinci a watan azumin Ramadan daya gabata, amma aka samu wasu suka yi awon gaba da ita.
Muhyi, yace sun samu nasarar kama daya daga cikin wadanda ake zargi da hannu a sace shinkafar, tare da alkawarin fadada bincike don gano sauran masu hannu a wannan badakala.
Muhyi ya tabbatar da cewa, buhunan shinkafar kimanin tirela 28 ne yayin da kowacce tirela ke dauke da buhu 600.
Ya kara da cewa a jikin shinkafar akwai sunan shugaban kasa Bola Tinubu kuma an rubuta cewa ba ta sayarwa ba ce, amma an samu an sauya buhun da wani buhun shinkafa mai suna Big Mama Rice Premium Quality, yayin da wasu kuma an saka musu buhun Elephant Classic Parboiled Rice.
Muhyi ya bayyana cewa, za a mika bayanan da hukumar ta tattara ga gwamna Abba Yusuf, domin daukar matakin da ya dace.