Kungiyar Kanikawa masu gyaran motoci ta kasa (NATA) reshen jihar Kano tace kaso 40 cikin 100, na mambobinta sun rasa aikin su daga lokacin da gwamnatin tarayya ta cire tallafin man fetur zuwa yanzu.
Shugaban kungiyar reshen Kano Yahya Ibrahim, ya bayyana damuwar sa sosai dangane da mummunan tasirin da cire tallafin man ya yiwa masu sana’ar kanikanci, yana mai cewa sun shiga kunci saboda karancin samun aiki daga masu ababen hawa.
:::Kotu ta bawa EFCC umarnin tsare Yahaya Bello zuwa ranar 10 ga Disamba
A don haka ya yi kira ga gwamnatin jihar Kano da ta shiga lamarin nasu tare da bayar da tallafi na taimaka wa kanikawan.
Cikin wata sanarwa da jami’in yada labaran kungiyar Rabi’u Kura, ya fitar yace kaso 40, na yayan kungiyar kanikawan motoci sun rasa aikin yi a yanzu haka.