Kudirin yin gyara a dokar haraji ta Nigeria wanda shugaban kasar ya aikewa majalisun dokokin kasa ya tsallake karatu na biyu a zauren majalisar dattawa, lokacin zaman ta na yau Alhamis.
:::Yau ake cika shekaru 10 da kai harin Boko Haram na Masallacin masarautar Kano
Kudirin dokar ya kasance mai cike da cece-kuce da kuma fuskantar kalubalanta musamman daga yan arewacin Nigeria, dake ganin kudirin a matsayin barazana ga yankin.
Dokar da ake son yiwa kwaskwarima ta kunshi fanni hudu da sabbin kidire-kudire, kuma ya tsallake karatun na biyu bayan yan majalisar sun yi mahawara akan sa, bayan gabatar da bukatar hakan daga Sanata Opayemi Bamidele, na jam’iyyar APC, daga jihar Ekiti.