Sojoji sun kashe kwamandan Boko Haram a jihar Yobe

0
62

Sojojin Nigeria dake karkashin atisayen Haɗin Kai tare da haɗin gwiwar ’Yan Banga, sun yi nasarar daƙile wani harin da mayakan kungiyar Boko Haram suka kai unguwar Sabon Fegi da ke Buni Yadi a Ƙaramar Hukumar Gujba ta Jihar Yobe.

Wani mai sharhi a kan lamuran tsaro a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makamai, ya sanar da cewa wasu majiyoyi sun shaida masa cewa an kai harin da misalin karfe 11 na daren alhamis data gabata.

Hudu daga cikin maharan sun gamu da ajalin su yayin harin, cikin su har da wani Kwamandan kungiyar Boko Haram, mai suna Abu Shekau.

Wani mazaunin garin Buni Yadi, da ya nemi a sakaye sunansa, ya bayyana cewar dakarun soji sun taka rawar gani wajen kisan yan ta’addan Boko Haram din.

Dakarun sojin sun yi nasarar daƙile harin ta hanyar hana mayaƙan Boko Haram shiga wajen da suke son aiwatar da mummunan shirin su.

Sojojin sun kuma ƙwato makamai da dama daga hannun mayakan.

Abu Shekau, wanda yake mai ra’ayi irin na tsohon shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau, ana ɗaukarsa a matsayin babban jigo a cikin ƙungiyar.

Abu Shekau, ya sanya wa ɗansa sunan Abubakar Shekau a matsayin girmamawa ga tsohon shugaban ƙungiyar Boko Haram.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here