Mun fara ganin amfanin cire tallafin man fetur a Nigeria—-Tinubu

0
64
Tinubu
Tinubu

Shugaban Nigeria Tinubu, yace a baya yan kasar sunyi rayuwa mai dadi amma ta bogi, wadda zata jefa kasar zuwa durƙushewa saboda biyan tallafin man fetur da gwamnatocin baya suka yi.

Yace haka ne yasa gwamnatin sa cire tallafin man fetur, a ranar 29 ga watan Mayu na shekarar 2023, Lokacin rantsar da shi.

Yace ya cire tallafin man fetur saboda ya tseratar da Nigeria daga durƙushewa kuma hakan bazai yiwu ba har sai an dauki mataki mai tsauri, daya kunshi cire tallafin fetur dana canjin kudaden ketare.

Tinubu, ya bayyana hakan a lokacin taron yaye dalibai na jami’ar tarayya ta Fasaha dake Akure, karo na 34.

Shugaban jami’ar Ilorin, Farfesa Wahab Egbewole, ya bayyana hakan sakamakon cewa shine ya wakilci Tinubu a taron.

Yace gwamnatin sa tana sane da irin kuncin rayuwa da mutane ke ciki saboda manufofin gwamnatiin sa, amma babu yadda za’a yi a cewar sa dole ayi hakuri, yana mai cewa zuwa yanzu sunga amfanin cire tallafin.

Tinubu, yace wannan wahala da ake sha itace zata bayar da damar gina rayuwar yara masu tasowa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here