Gobara ta kone shaguna masu yawa a Damaturu

0
46

Tashin wata mummunar gobara yayi sanadiyyar konewar akalla shaguna 20, na siyar da kayayyakin mata a kasuwar bayan tasha a garin Damaturu, na jihar Yobe.

Rahotanni sun bayyana cewa gobarar ta sanya anyi asarar miliyoyin kudi, wadda ta tashi da misalin karfe daya na daren ranar litinin.

:::Babu gaskiya a zaton cutar da arewa a dokar haraji—Fadar Shugaban kasa

Gobarar ta fara tashi daga wani shago da ake sana’ar siyar da hijabi na mata sannan daga bisani ta fantsama zuwa sauran shaguna, kamar yadda wani da lamarin ya faru a gaban idon sa ya shaidawa jaridar Aminiya.

Bayan tashin gobarar ne wata tukunyar iskar gas ta fashe, lamarin da ya watsa wutar zuwa wasu shaguna da ke kasuwar.

Hukumar Kashe gobara ta jihar Yobe tace jami’an ta sun yi nasarar kashe gobarar akan lokaci bayan samun kiran gaggawar da akayi musu.

Wannan dai ba shi ne karon farko ba da ake samun tashin gobara a kasuwar, wadda lokaci zuwa lokaci a kan samu faruwar irin wannan iftila’i, wanda wasu ke alakantawa da sakacin wasu ’yan kasuwar da ke barin kayayyakin da ke amfani da wutar lantarki a kunnen bayan sun tashi daga kasuwar.

Wasu kuma na alakanta gobarar da cinkoso a kasuwar wanda masu ra’ayin hakan suk ce na haifar da yawaitar tashin gobara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here