Sanata Barau yakai kudirin samar da jami’a mai sunan Yusuf Mai Tama a Kano

0
85

Sanata Barau I Jibril, dake wakiltar arewacin Kano, a zauren majalisar dattawa, Kuma mataimakin shugaban majalisar yakai kudirin neman samar da wata sabuwar jami’ar gwamnatin tarayya a Kano, mai sunan Yusuf Mai Tama Sule.

Kamar yadda wata sanarwa ta fita Barau, ya gabatar da kudirin neman Samar da jami’ar da sanya mata wannan don a rika tunawa da irin gudunmuwar da Marigayi Yusuf Mai Tama Sule (Dan masanin Kano) ya bawa al’umma a lokacin rayuwar sa.

Wannan lamari, yazo yan kwanaki bayan da gwamnatin Kano, ta sauya sunan jami’ar ta YUMSUK, zuwa sunan ta na asali wato North West, inda gwamnatin tace zata samar da wata kwaleji da za’a sakawa sunan Yusuf Mai Tama Sule.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here