A karon farko cikin tarihin kasuwar crypto, a yau alhamis 5/12/2024 an samu gagarumar nasara inda kowanne Bitcoin daya darajar sa ta zarce Dala dubu 104,087, sannan ta zarce naira miliyan 176,947,900, a kudin Nigeria.
Hakan baya rasa nasaba da nasarar Donald Trump, ta lashe zaben shugaban kasar Amurka, zaben 5 ga Nuwamba, wanda tun lokacin farashin Bitcoin yake tashi babu tsayawa.
Trump, ya kasance mai goyon bayan harkokin kasuwancin Crypto, yayin da Kamala Harris, da suka yi takara tare bata goyon bayan harkokin crypto.
Dama anyi hasashen cewa in har Trump, ya lashe zaben shugaban kasar Amurka, kasuwar crypto zata samu alkairi masu yawa, saboda yayi alkawarin taimakawa crypto, kuma shima daya ne daga cikin manyan yan crypto na duniya.
Daga yanzu zuwa ko yaushe za’a iya ganin darajar kowanne Bitcoin daya ta zarce darajar da mutane ke tunani.
Ana hasashen cewa harkokin crypto zasu cigaba da samun nasara har bayan rantsar da Donald Trump, a matsayin shugaban Amurka a watan Junairu na 2025.
A halin yanzu ana samun sabbin masu zuba hannun jari a kasuwar ta crypto saboda tagomashin alkairin da ake samu.
Suma sauran coins da ba Bitcoin, ba sun fara mikewa, musamman yadda darajar Ethereum, daya ta zarce Dala dubu uku da dari takwas.