Majalisar dokokin Kano, na duba yiwuwar yin gyara a cikin dokar hukumar kashe gobara ta jihar da aka samar a shekarar 1970.
Za’a yi gyaran a doka mai lamba 17, da manufar samar da wani sashin da zai kula da karuwar bude guraren siyar da iskar Gas din girki a cikin al’umma barkatai ba tare da kula da illolin da hakan ka’iya haifarwa ba.
Kwamitin kula da ayyuka na majalisar ne ya gabatar da wani rahoton sa ga zauren majalisar, lokacin zaman da kakakin majalisar dokokin Kano Hon. Ismail Falgore ya jagoranta, wanda rahoton yayi duba akan bude guraren siyar da Gas a unguwanni.
Wakilin karamar hukumar Gezawa, a majalisar Abdullahi Yahaya, wanda shine shugaban kwamitin, ya bayyana cewa, hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta bayar da rahoton kimanin gidaje 475 na masu sayar da iskar gas da suka aiwatar da Sana’ar su ba bisa ka’ida ba.
Ya kuma kara da cewa, alkaluman da hukumar sa ido kan harkokin man fetur ta kasa, reshen jihar Kano ta fitar ya nuna cewa, akwai masu sayar da iskar gas guda 234 da ba su da lasisi a jihar.
A cewarsa, an gudanar da binciken ne biyo bayan wani kudiri da dan majalisa mai wakiltar mazaɓar Kiru, Hon. Tasiu Abubakar ya gabatar game da hatsarin da ke tattare da sayar da iskar gas a cikin al’umma da kuma buƙatar samar masu wasu keɓaɓɓun wurare domin kiyaye rayuka da dukiyoyin al’umma.
Sai dai kwamitin ya ba da shawarar cewa, ya kamata gwamnatin jihar ta samar da wurin dindindin.