Shugaban kamfanin mai na Nigeria Mele Kyari, ya tabbatarwa da yan kasar cewa matatar an fetur ta Fatakwal tana aikin tace mai yadda ya kamata.
Kyari, ya sanar da hakan a ranar larabar data gabata, yana mai cewa sun himmatu wajen habbaka fannin tace man fetur a cikin gida, tare da yin watsi da kalaman masu cewa matatar ba za’a yi wani abun kirki ba wajen tace albarkatun mai.
:::Tsaffin sojojin Nigeria sun yi zanga-zangar neman hakkin su a wajen gwamnati
Shugaban na NNPCL, yace maganar fara tace man fetur a matatar Fatakwal ba kanzon kurege bane magana ce ta gaskiya, wanda a yanzu tana kan aiki kuma motoci suna kan aikin dakon mai daga matatar a yanzu haka, sannan ana tace duk abin da muka sanar tun da farko, bayan haka zamu fara fitar da man zuwa kasuwa.
Kyari, ya kuma yi nuni da cewa NNPCL, yana kan kokarin ganin ya gyara duk wasu matatun man da suke mallakin gwamnati, a nan kusa.
Wadannan kalamai na Mele Kyari, zasu iya kasancewa a matsayin martani ga mutane dake cewa NNPCL, ya yiwa yan Nigeria karya a maganar fara tace fetur a matatar Fatakwal, inda wani bincike ya nuna cewa ko inji daya baya yin aiki a matatar bayan NNPCL, ya fitar da sanarwar fara aikin matatar ta Fatakwal.