Hukumar kula da ayyukan rundunar yan sandan Nigeria PSC, ta sanar da korar jami’an yan sandan guda 19, daga aiki a yau juma’a, inda tace ma’aikatan an kore su saboda aikata mummunan laifin daya sabawa ka’idojin aikin su.
Hukumar ta yanke wannan hukunci lokacin data gudanar da wani taro a birnin tarayya Abuja, karkashin jagorancin Shugaban hukumar Hashimu Argungu, wanda a zaman aka kuma ragewa wasu ma’aikatan su 19 matsayi zuwa kasa, bayan suma an same su da karya ka’idar aiki.
Yan sandan da aka kora sun hadar da masu mukamin ASP su 10, sai masu mukamin CSP su 6, da masu mukamin DSP 2, sai SP 1.
Daily trust, ta rawaito cewa an dauki matakin bayan hukumar kula da ayyukan yan sandan ta karbi rahoton binciken ma’aikatan daga kwamishinonin yan sandan jihohin su.
Mai magana da yawun, hukumar Ikechukwu Ani, yace an hukunta yan sanda masu mukamin AIG, su biyo saboda bijirewa umarnin aikin da aka basu.