Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi na II, yace akwai masu tayar da hankalin al’umma a jihar Kano.
Yace wasu mutane suna nan burin su shine a zubar da jini a Kano.
Sarkin, ya bayyana hakan a yau lokacin da yake gabatar da hudubar Sallar juma’a, a Masallacin cikin gari.
Kalaman nasa basa nasaba da girke jami’an tsaro a Masarautar Kano don hana shi halartar taron nadin sarautar hakimin Bichi.