Wasu yan ta’adda sun kai farmaki ga mahaifiyar Gwamnan jihar Taraba, da yar uwar sa, lokacin da suke kokarin zuwa wani uzuri a karamar hukumar Wukari.
Mahaifiyar tasa mai suna Jummai, da kanwar gwamnan Bari Atsi, sun fuskanci harin a ranar juma’a yayin da suke tafiya a yankin Wukari Kante, cikin karamar hukumar Wukari.
Jaridar Daily trust, ta rawaito cewa shugaban karamar hukumar ta Wukari, ya tabbatar da afkuwar lamarin yana mai cewa maharan sun zo a babura masu kafa biyu sannan suka yi kokarin tsayar da motar dake dauke da dangin gwamna Agbu Kefas.
A yayin harin yar uwar gwamnan ta samu rauni sakamakon harbin bindiga, da a yanzu haka take karbar magani.
Rahotanni sun bayyana cewa daya daga cikin jami’an tsaron dake tare da mahaifiyar Gwamnan yayi kokarin yin harbi a iska don tsorata maharan da har yanzu ba’a san su waye ba.