Mayakan tawayen Syria sun sanar da kwace babban birnin kasar Damascus, daga hannun jami’an gwamnati, bayan kwashe shekaru ana rikici tsakanin jami’an Gwamnati masu goyon bayan Bashir Al Assad, da yan tawayen.
Shugaban yan tawayen Abu Mohammed al- Jawlani ya bayyana nasarar kwace birnin a matsayin babban tarihi, tare da kira ga mayakansa kar su cutar da duk wanda ya mika musu wuya.
Tun da farko ‘yan tawayen sun ce sun kama birnin Homs, wanda shi ne birni na uku mafi girma a Æ™asar.
Daman wani rahoton na cewa ‘yan tawayen sun ce sun shiga babban birnin, Damascus, kuma Shugaba Bashar al-Assad ya tsere ba a san inda yake ba.
Rikicin Syria, dai ya yi sanadiyyar mutuwar mutane babu adadi wanda basu ji ba basu gani ba.