An yi yarjejeniyar zaman lafiya da yan ta’addan Birnin Gwari

0
51

Gwamnatin jihar Kaduna, jami’an tsaro da sauran al’umma sun yi taron sasanci da zaman lafiya da yan bindigar dake addabar mutane a karamar hukumar Birnin Gwari.

Karamar Hukumar Birnin Gwari, dai tayi kaurin suna wajen fuskantar hare haren yan ta’adda da sauran ayyukan rashin tsaro tsawon lokaci.

Sai dai a yanzu abubuwa sun fara komawa daidai yayin da al’ummar yankin suka fara samun zaman lafiya biyo bayan wata yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma da masu tayar da hankalin al’umma.

Wannan yarjejeniya ta kawo farin ciki ga mutanen yankin saboda sun sha fama da hare hare da rashin nutsuwa.

An shafe shekaru da dama ’yan bindiga na addabar mutanen yankin da ke zaune a ƙauyuka daban-daban, lamarin da ya yi sanadiyar rasa rayukan da dukiyoyi masu yawan gaske musamman gonaki tare da tarwatsa wasu mazauna yankin daga garuruwansu.

Noma wanda shi ne babbar sana’a ga al’ummar yanki ya samu koma baya sakamakon hare-haren da ’yan bundiga ke kai wa manoma a gonakinsu.

Sannan akwai manoma da yawa da ke hannun ’yan bindigar suna jiran danginsu su biya kudin fansa kafin a sako su.

Daya daga cikin shugabannin yankin Kwasakwasa mai suna Malam Abu ya bayyana cewa haƙiƙa an fara samun kwanciyar hankali a yankin su da ƙauyen Sabuwar Kuyello.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here