Gwamnatin tarayya ta nesanta kanta daga jerin wasu sunaye masu yawo a shafukan sada zumunta da ake cewa itace ta fitar da su a matsayin mutanen da zata tura jakadanci zuwa kasashen duniya.
Gwamnatin tace ko kadan hakan ba gaskiya bane, Kuma bata fitar da sanarwar nadin wasu Jakadu ba.
Ma’aikatar harkokin waje ta kasa ce ta bayyana cewa jerin sunayen na karya ne.
Ma’aikatar ta bukaci al’umma su yi watsi da sunayen inda ta ce shugaban kasa ne kadai zai iya nada jakadun Najeriya na kasashen waje.