Dan shekara 22 ya kashe mahaifiyar sa da wuka

0
177

A jihar Bayelsa dake kudancin Nigeria wani matashi ne ya kashe mahaifiyar sa.

Matashin mai suna Godwin, ya kashe babar tasa ta hanyar caka mata wuka a karamar hukumar Ogbia, ta jihar Bayelsa, saboda yana zargin ta cewa ita ta hana shi yin arziki a rayuwar sa.

Matashin dan asalin jihar Bayelsa ya kasance mai yin rayuwa a jihar Edo, wanda ya koma gida kwanaki kadan da suka wuce.

:::Shugaban kasar Jamus zai shafe kwanaki uku a Nigeria

Mazauna unguwar da abin ya faru sun ce wani malamin coci ne ya umarci mahaifiyar Godwin da kar ta sake ta karbi duk wata kyautar da dan nata zai kawo mata.

Wasu kuma sun ce Godwin, ya dawo gidan da wasu halaye, inda yake iƙirarin cewar an ce mahaifiyar ce ta hana shi yin arziƙi.

Shugaban matasan unguwar Elebele, Kwamared Precious Okala, ya ce lokacin da suka isa wajen, sun tarar da gawar mahaifiyar cikin jini, yayin da matasan unguwar suka kama Godwin suka É—aure shi.

Kakakin ‘yan sandan jihar, ASP Musa Mohammed, ya ce an miƙa lamarin zuwa sashen binciken manyan laifuka (SCID) don ci gaba da bincike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here