Mai shara a asibiti ya mayar da naira miliyan 40 daya tsinta zuwa ga mai kudin a Kano

0
67

Wani ma’aikacin jihar Kano, dake yin shara a asibitin kula da masu matsalar mafitsara na Abubakar Imam Urology, ya tsinci wasu makudan kudade da yawan su yakai naira miliyan 40.

Mutumin mai suna Aminu Umar, ya tsinci kudaden a dalolin kasar Amurka, da aka manta dasu a cikin wata jaka a Asibitin na Abubakar Imam da ke karamar hukumar Fagge.

Malam Aminu wanda matsakaicin ma’aikaci ne ya tsinci kudin a cikin wata jaka kuma ya mayar da kudin ga mamallakin su mai suna Alhaji Ahmed Abubakar, wanda ya manta da su a lokacin da ya je dubiyar mara lafiya a asibitin.

Alhaji Ahmed ya manta da kudin ne a wurin da ya zauna na dan lokaci a wurin ajiye motoci da ke kusa da masallaci, inda daga bisani ya wuce domin shiga jirgin sama domin yin tafiya.

Malam Aminu ya shaida wa wakilin Aminiya cewa, jim kadan da tafiyarsa mutumin ne shi kuma ya tsinci kudin a lokacin da yake aikin shara.

Ya ce daga bisani, bayan kimanin awa guda, mai kudin ya dawo kuma ya mayar masa kayansa.

Ya ce mai kudin ya yi masa kyauta amma ya ki amsa, duk da cewa ya ba shi lambar wayarsa, kuma mutumin ya yi alkawarin tuntubar sa idan ya dawo daga kasar waje.

Shugaban Asibitin, Dakta Aminu Imam Yola, ya tabbatar da faruwar lamarin yana mai cewa hukumar gudanarwar asibitin ta sanar da hukumar Kula da Asibitoci ta Jihar Kano domin a karrama Malam Aminu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here