Gobarar kasuwar Alaba Rago ta haifar da asara a jihar Lagos

0
59

An wayi gari da ganin iftila’in tashin gobara a kasuwar Alaba Rago, dake jihar Lagos, a yau laraba.

Rahotanni sun bayyana cewa tashin gobarar ya haifar da asarar miliyoyin kudi kamar yadda aka sanar cikin wata sanarwa da hukumar agajin gaggawa ta jihar ta fitar inda ta ce gobarar ta tashi a cikin daren Laraba.

Sai dai sanarwar bata bayyana dalilin tashin gobarar ba kawo yanzu.

Dr Femi Oke-Osayintolu, shine sakataren hukumar bayar da again gaggawa ta Lagos wanda yace jami’an hukumar sun isa kasuwar da wuri bayan kiran wayar da aka rika yi musu daga kasuwar.

Ya ce, koda isar jami’an nasu sun tarar wutar ta fara cin shaguna.

Yace suma jami’an hukumar kashe gobara sun isa wajen akan lokaci tare da kokarin kashe wutar kafin wani mummunan matakin da ba’a tunani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here