Mayakan Boko Haram sun yanka masu kamun kifi su 14 a iyakar Najeriaya da Nijar

0
65
ISWAP BOKO HARAM
Boko Haram ISWAP

Wasu masu sana’ar kamun kifi a yankin Diffa na jahuriyar Nijar su 14 sun gamu da ajalin su a hannun yan ta’addan Boko Haram.

Mayakan na boko haram sun kashe masu kamun kifin ta hanyar yi musu kisan gillar yankan rago tare da fille kawunan su.

:::Jirgin sama ya sauka daga titin sa bayan tayar sa ta fashe a Abuja

Tunda farko mutanen da aka kashe din sun kasance yan Nigeria da suka gujewa rikicin boko haram daga jihohin arewa maso gabas don komawa Nijar su cigaba da yin sana’a.

  • An kai musu harin ne yayin da suke kamun kifi a kusa da Bosso a ranar Lahadi.

Shugaban ƙungiyar ’yan sa-kai da ke taimaka wa sojojin Najeriya, Babakura Kolo, ya ce ’yan ta’addan sun sare wuyan masu kamun kifin su 14.

Mutanen da aka kashe sun fito daga yankin Malam Fatori da Doron Baga na Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here