Babban turken wutar lantarkin Nigeria ya lalace karo na 12 cikin shekarar 2024, da hakan ta faru da misalin karfe 1:33, na rana a yau laraba.
Wani ma’aikacin fannin lantarki a Nigeria shine ya tabbatar da lalacewar wutar a shafin sa na X, da misalin karfe 2:09 na rana, sannan yace a yanzu haka jami’ai suna kan gyara matsalar lalacewar lantarkin.
:::NAFDAC ta lalata jabun magani da kudin sa zarce naira biliyan 10
Bayan haka kamfanin rarraba lantarki na Jos shima ya tabbatar da lalacewar wutar.
A cikin wannan shekara ta 2024, an samu lalacewar lantarki da ba’a taba fuskantar ta ba a tarihin Nigeria sakamakon lalacewar babban turken wutar har sau 12 cikin watanni 12.