Yan tawayen Syria sun kona kabarin mahaifin Bashar Al Assad

0
48

Yan tawayen da suka kifar da Gwamnatin tsohon shugaban kasar Syria Bashar Al Assad, sun kone kabarin mahaifin sa, wanda shima tsohon shugaban kasar ta Syria ne a lokacin da yake raye.

Wasu hotuna daga yankin Lakatia, sun nuna yan tawayen a tsaye yayin da wata akwatin da gawar mamacin ke ciki, da ake kyautata zaton cewa an fito da ita ne daga kabarin ke ci da wuta.

A shekarar 2000 ne mahaifin Bashar al-Assad ya rasu, inda aka binne shi a wani wuri na musamman a ƙauyensu,, Qardaha.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here