Gwamnoni sun goyi bayan samar da yan sandan jihohi

0
46

Gwamnonin Nigeria sun nuna amincewar su da tsarin samar da yan sandan jihohi wanda tun a baya ake cece kuce akan samar da yan sanda musamman saboda tabarbarewar harkokin tsaro.

A jiya alhamis gwamnonin sun gudanar da wani taro na majalisar tattalin arzikin kasa karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, a fadar shugaban kasa dake birnin tarayya Abuja.

Mafi yawa daga cikin gwamnonin sun halarci taron yayin da wasu mataimakan gwamnonin suka wakilce su.

Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani, bayan kammala taron ya bayyanawa manema labarai cewa suna goyon bayan samar da yan sandan jihohin.

Uba Sani, yace kowacce jiha tana da irin nata matsalar tsaron da ya kamata a amincewa samar da yan sandan da zasu samu nasarar magance su.

To sai dai majalisar ta jingine tattaunawa kan batun samar da yan sandan jihohin zuwa watan Junairu na shekara mai kamawa.

An dai jima ana batun amincewa jihohin Nigeria su samar da yan sanda nasu na kansu, wanda wasu ke goyon bayan hakan wasu kuma ke kalubalantar tsarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here