Ma’aikatan hukumar samar da ruwan sha sun fara yajin aiki a jihar Kano

0
58

Ma’aikatan hukumar samar da ruwan sha ta jihar Kano sun fara yajin aikin sai baba ta gani, saboda gazawar gwamnatin jihar wajen fara biyan su mafi karancin albashin ma’aikata na naira dubu 70, da aka fara biya a watan Nuwamba.

Shugaban kungiyar ma’aikatan Malam Najib Abdussalam, ne ya sanar da hakan, inda yace kafin yanzu sun tattauna da shugaban hukumar samar da ruwan sha ta jihar Kano Ahmad Garba Bichi, akan batun fara biyan mafi karancin albashin kafin watan Disamba.

Najib, ya tabbatar da cewa sun tattauna da hukumar tare da yin yarjejeniyar biyan mafi karancin albashin, duk da cewa hukumar tana tattara kudaden shigar da bazai bayar da damar fara biyan su mafi karancin albashin ba.

Shugaban hukumar samar da ruwan Engineer Ahmad Bichi, yace za’a yi wa ma’aikatan karin albashi bayan an kara kudin ruwan da hukumar ke karba.

Tuni dai aka dena aiki a matatar ruwa ta Challawa, yayin da ake yin gyara a matatar ruwa ta Tamburawa.

Zuwa yanzu dai ana siyar da ruwa na jarka nai nauyin kilogram 25 naira 100 a wasu unguwannin jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here