Farashin Wake ya karye a kasuwannin jihar Lagos

0
45

Masu kasuwanci da magidanta sun nuna farin cikin su bisa karyewar farashin wake a kasuwannin jihar Lagos dake kudancin Nigeria.

Yan kasuwar sun bayyana farin cikin nasu a jiya lokacin da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya zanta dasu.

Rahoton kamfanin dillancin labarai NAN, ya nuna cewa an samu raguwar farashin waken a cikin watannin da suka wuce zuwa yanzu.

A watannin baya an siyar da buhun wake mai kilo 100 akan naira dubu dari da hamsin wanda a yanzu ake siyarwa akan naira 140.

Haka zalika akwai wanda aka siyar kan naira dubu dari da ashirin yanzu ya koma dubu dari.

Wani dan kasuwar dake siyar da wake mai suna Yakubu Ahmad, yace raguwar farashin baya rasa nasaba da girbin amfanin gona da akayi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here