An nada shugaban kasa na rikon kwarya a kasar Koriya ta Kudu

0
42

Mahukuntan kasar Koriya ta Kudu sun tabbatar da naɗin firaministan kasar a matsayin shugaban ƙasa na riko bayan da majalisar kasar ta tsige shugaban kasar Yoon Suk Yeol.

Shugaban na riko Han Duck-so, yace zai yi kokarin dawo da komai daidai a kasar tare da kwantar da hankalin al’umma, kamar yadda ya bayyana a jawabin sa na farko bayan zama shugaban Koriya ta Kudu.

Yan majalisar dokokin kasar sun tsige Yoon Suk Yeol, sakamakon wata takaddama data taso kan dokar fannin sojin kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here