Shalkwatar tsaron kasa ta ce ko kadan babu gaskiya a labaran da ake yaÉ—awa na cewa dakarun sojojin Faransa na shirin kafa sansani a arewacin Najeriya.
Wata sanarwar da daraktan yaÉ—a labaran shalkwatar Manjo Janar Edward Buba ya fitar a yau Litinin ta ce labaran jita-jita ce, kuma ba gaskiya bace.
Sojin sun ce sun gano labaran da ake yadawa a kafafen sada zumunta masu nuni da cewa sojojin Faransa sun fara kafa sansani a jihar Borno, tare da yada cewa akwai karin wasu dakarun na Faransa da za’a kawo Nigeria har akai ga kafa musu sansani a arewa maso gabashin kasar nan.
Rundunar sojin ta Kuma tabbatar da cewa wannan rahoto na ƙarya ne kuma bashi da makama.
Idan za a iya tunawa babban hafsan Najeriya, Janar Christopher Musa, ya yi bayani game da wannan batu, kuma ya jaddada cewa jita-jita ne kawai aka kitsa.