Cibiyar kididdiga ta kasa NBS, tace hauhawar farashin kayan masarufi takai kaso 34.6, a watan Nuwamba wanda aka samu kari akan kaso 33.8, na watan Oktoba.
Cibiyar ta fitar da alkaluman hauhawar farashin ne a yau litinin, inda tace an samu karin kaso 0.72, daga Oktoba zuwa yau.
:::Gwamnan Kano ya aikewa majalisa sunayen kwamishinoni 6 ciki har da Sagagi
A yanayin shekara kuwa an samu karin kaso 6.4, idan aka kwatanta da watan Nuwamban shekarar 2023.
A cewar NBS farashin kayayyakin abinci ya tashi zuwa kaso 39.93 a wannan shekarar, wanda yake akan matsayi na kaso 32.84, a shekarar 2023, karuwar farashin kayan abincin yafi yawa akan Doya, Ruwan sha, Masara, Shinkafa, da kuma man girki.
Jihar Bauchi itace kan gaba a jerin jihohin da aka fi samun tashin farashin kayayyakin sai Kebbi, da Anambra.
Jihohin da aka samu saukin kayan kuwa su ne Katsina, Benue, da Delta.