Nigeria zata ciyo bashin naira triliyan 13 na cike gibin kasafin shekarar 2025

0
44

Gwamnatin Nigeria ta sanar da shirin ta na ciyo bashin naira triliyan 13 da tace za’a yi amfani da su wajen cike gibin kasafin kudin shekarar 2025, mai kamawa.

Ministan kudi Wale Edun, ne ya sanar da cewa zasu nemi bashin naira tiriliyan 13 don cike giɓin da ke cikin kasafin.

Ya bayyana hakan a jiya bayan kammala taron majalisar zartarwa ta tarayya, da Tinubu, ya jagoranta, inda Wale Edun, yace basu da wani zabin daya wuce ciyo bashin don tabbatar da aiki da kasafin kudin ba tare da samun matsala ba.

Jumular kuɗin gudanar da ayyuka da ke cikin kasafin ya kai naira tiriliyan 34 da biliyan 8 daga cikin ƙunshin kasafin na naira tiriliyan 47 da biliyan 9 wanda ke nuna ƙaruwar kashi 36.8 daga kasafin 2024.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here