Naira ta cigaba da samun tagomashi akan Dalar Amurka

0
72
Farashin Dala zuwa naira
Farashin Dala zuwa naira

Takardar kudi ta naira na cigaba da samun tagomashi tare da farfadowa akan dalar Amurka idan aka kwatanta da makonnin baya.

A jiya litinin a kasuwar bayan fage an sauya kowacce dala daya akan naira 1660, sabanin naira 1662, da aka sauyar da dalar a karshen mako.

:::Gwamnatin tarayya zata gina sabbin tashoshin lantarki 5

Sai dai a kasuwar gwamnati takardar naira ta samu koma baya zuwa dala daya da aka sauyar akan naira 1550.

Wasu alkaluman da aka samu daga hukumar kula da sauyin kudaden ketare sun bayyana cewa a karshen mako an sauyar da dala daya akan naira 1540, wanda aka samu karin naira 10, kan kowacce dala daya a jiya litinin zuwa naira 1550 akan kowacce dala.

A kusan makonni biyu zuwa uku ana samun hawa da sauka tsakanin naira da dala, wanda naira tafi samun tagomashi, sakamakon a wata daya daya gabata ana sauyar da dala daya akan naira 1750.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here