Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya kare kudirin dokar sauyin fasalin harajin da yake so a aiwatar a kasar nan wadda take cike da cece-kuce.
Ya jaddada cewa wannan doka da ake nunawa kyama musamman daga yankin arewa an samar da ita ne don inganta fannin tattarawa Nigeria Kudin shiga.
:::Naira ta cigaba da samun tagomashi akan Dalar Amurka
Haka zalika Tinubu, ya nemi a hannu tsakanin bangaren zartarwa da majalisun dokokin kasa don ciyar da Nigeria gaba a kowanne lokaci.
Tinubu, ya sanar da hakan yayin daya halarci taron tunawa da Sanata Abiola Ajimobi, karo na 7, wanda ya gudana a ranar litinin, kuma an aiwatar da bikin a jami’ar Ibadan, wanda Daraktan cibiyar sasanci ta kasa Dr Joseph Ochoku, ya wakilci shugaban kasar.
Gidauniyar tunawa da Abiola Ajimobi, ce ta shirya taron tare da cibiyar samar da sasancin ta kasa.
Dr Joseph Ochoku, yace shugaban kasa Tinubu, ya nuna jajircewa tare da nuna sha’awar yin aiki tare daga majalisar zartarwa zuwa majalisun dokokin kasa, yana mai cewa in har majalisa ta amince da dokar harajin za’a samar da rabon tattalin arzikin kasa ba tare da fifita wani bangaren Nigeria ba, tare da cewa hakan zai janyo hankalin masu zuba hannun jari daga waje zuwa Nigeria