A yau Laraba ake kyautata zaton shugaban Nigeria Bola Tinubu, zai gabatarwa da majalisun dokokin kasa kasafin kudin shekarar 2025.
Da farko shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio, ya sanar da ranar talata data gabata a matsayin lokacin da shugaban zai gabatar da kasafin, amma daga baya aka samu sanarwar sauya lokacin zuwa yau Laraba.
Kamar yanda aka kiyasta kasafin kudin Nigeria na shekarar 2025, zai kaiwa naira triliyan 48, wanda kudin ya kunshi naira triliyan 13, da za’a ciyo bashin ta don cike gibin kasafin.
Ministan kudi Wale Edun, shine ya sanar da shirin gwamnatin na ciyo bashin da za’a cike gibin kasafin.