Kamfanin NNPCL ya ciyo bashi saboda matatar Dangote

0
118

Kamfanin mai na NNPCL ya bayyana cewa ya karbo bashin dala biliyan 1, da manufar taimakawa aikin samar da matatar man fetur ta Dangote a lokacin da aikin gina matatar ya fuskanci karancin kudi.

Kakakin kamfanin, Olufemi Soneye, ya sanar da hakan lokacin da yake jawabi a wani taron masana harkokin makamashi daya gudana a birnin tarayya Abuja.

Sonoye, yace manufar karbo bashin itace a taimakawa yunkurin samar da matatar don aiwatar da ita ba tare da samun tangarda ba.

A cewar sa bayar da wannan tallafi ya bayar da damar buɗe ƙofa ga matatar mai ta farko mallakar ‘yan kasuwa a Najeriya, wanda ke nuna ƙarfin gwiwar NNPC wajen tallafawa haɗin gwiwar gwamnati da ‘yan kasuwa don ci gaban ƙasa.

Ya kuma jaddada cewa ana sa ran Matatar Dangote za ta taka muhimmiyar rawa wajen rage dogaro da shigo da mai cikin Nigeria daga ƙasashen waje.

A cewarsa, matatar za ta ƙara yawan man da ake tacewa a cikin gida tare da bayar da gudummawa ga samar da makamashi da bunƙasar tattalin arziƙin ƙasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here