Majalisun dokokin kasa sun kara yawan kudin da za’a kashe a kasafin kudin 2025

0
49

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya gabatarwa da majalisun kasa kasafin kudin shekarar 2025.

Shugaban ya gabatar da kasafin ne ga mambobin majalisar dattawa data wakilai a zauren majalisar wakilai.

Adadin kudin kasafin yakai naira triliyan N47.96, da za’a cike gibin sa da bashin naira triliyan 13.

Ministan kasafi Atiku Bagudu, da ministan kudi Wale Edun, na daga cikin wadanda suka halarci taron gabatar da kasafin.
Cikakken bayani na nan tafe.

Tinubu, ya je majalisar da misalin karfe 12:12, na rana tare da tawagar sa, data kunshi, mataimakin sa Kashim Shettima, da sauran su.

A yayin jawabin sa shugaban majalisar dattawa Akpabio, ya nemi Tinubu, ya ja kunnen ministocin da suke kin amsa gayyatar majalisar.

Majalisar tace ta kara yawan kasafin kudin shekarar 2025, da kaso 50, cikin 100, tare da kara wa’adin yin amfani da kasafin kudin shekarar 2024, zuwa watan Yunin 2025.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here