Babban bankin kasa CBN yace daga yanzu masu hada-hadar kudi ta POS naira miliyan 1 da dubu dari 2, kawai zasu rika fitarwa a kowacce rana.
Bayanin hakan ya fito cikin wani umarni da babban bankin ya fitar ranar talata, kuma aka sanar ga wakilan bankuna masu harkallar kudade.
:::Shugaban kasa Tinubu ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2025
Oladimeji Yisa, shine ya sanar da hakan a adadin shugaban sashin tsare-tsare na bankin, yana mai cewa anyi hakan don rage amfani da tsabar kudade ga yan kasa.
Bayan haka daidaikun masu ajiya a bankuna basu da damar cire tsabar kudin daya zarce naira dubu dari 5, a kowanne mako.
Dama ba’a yi mamakin ganin wannan umarni ba musamman yanda ake fuskantar karancin kudade a hannun al’umma.
Masana harkokin tattalin arziki na ganin cewa ana yin irin wadannan sauye-sauye don samun kudaden shigar da gwamnati ke cira a lokacin da aka yi hada-hadar kudade ta bankuna, wanda hakan ba zai yiwu ba, in har da tsabar kudi akayi amfani.