Shugaban kasa Bola Tinubu, ya amince da wasu sauye sauyen mukaman shugabannin hukumar kula da tafkuna ta kasa, karkashin ma’aikatar albarkatun ruwa.
Mai Mai taimakawa shugaban a fannin yada labarai Bayo Onanuga, ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa daya fitar yau.
Sanarwar tace an nada Rabi’u Sulaiman Bichi, da musa Iliyasu Kwankwaso, a mukaman daraktocin hukumar kula da tafkin Hadejia Jama’are.
Mutanen biyu sun kasance tsaffin masu rike da mukamai a Gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje, lokacin yana matsayin Gwamnan Kano.