Matatar Dangote ta rage farashin litar man fetur

0
56
Aliko-Dangote
Aliko-Dangote

Matatar Dangote ta sanar da rage farashin litar man fetur zuwa naira 899.50 kafin zuwan bukukuwan kirsimati da sabuwar shekara.

Mai magana da yawun matatar Anthony Chiejina, shine ya sanar da cewa an rage farashin litar man ne domin rage tsadar sufuri ga jama’a, a lokacin Æ™arshen shekara.

Ko a cikin watan Nuwamba matatar man ta rage farashin litar mai zuwa naira 970.

Chiejina, yace saboda samar da sauƙi kan sufuri a lokacin hutun ƙarshen shekara, matatar mai ta Dangote ta fara sayar da mai a kan ragin farashin data sanar.

Chiejina ya jaddada cewa matatar ta jajirce wajen tabbatar da ganin an samarwa jama’ar Najeriya fetur mai inganci da sauki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here