Al’ummar da ministan birnin tarayya Abuja Nyesom Wike, ya bayar da umarni aka rushewa gine-ginen su sun bayyana cewa hakan ya jefa rayuwar su cikin kunci da tashin hankali.
Bayanin mutanen yazo a daidai lokacin da mahukuntan Abuja, ke cewa an rushe gurare 20,432, a shekarar 2024, yayin da al’umma ke cewa wannan aiki ya kasance cutarwa kuma bai kamata ayi hakan ba.
:::Kotu ta umarci gwamnatin Kano ta biya diyyar biliyan 8.5 ga wadanda ta rushewa Gini
Jaridar Daily Trust, ta rawaito cewa Wike, ya bayar da muhimmanci akan tattara kudaden shiga, ta hanyar biyan kudaden harajin gine-gine, da saubuta takardun mallakar filaye.
An bayar da rahoton cewa gwamnati ta kuma kwace wasu guraren da aka gina su ba akan ka’ida ba, tare da bayar da wa’adi ga wasu mutanen su bayyana shaidar mallakar guraren su kafin lokaci ya kure.
Sai dai kungiyar masu gina gidaje dake Sabon Lugbe, ta zargi gwanmati da son kwacewa mutane guraren su da gangan.
Kafin yanzu mambobin kungiyar sun zanta da Wike, akan rushe-rushen wanda hakan bai haifar da wani sakamako mai kyau ba.