Kaso 56 na al’ummar Nigeria suna burin barin kasar–Rahoto

0
39

Wani rahoto da jaridar Guardian, ta fitar ya nuna cewa kaso 56, na yan Nigeria suna da burin barin kasar, da haka ya zama an samu karin kaso 20 cikin wadanda ke burin barin kasar idan aka kwatanta da shekarar 2017, da kaso 36 na mutane ke son barin kasar.

Cibiyar bincike ta Afrobarometer, ce ta bayyana hakan, inda tace masu son barin kasar sun hadar da masu sha’awar zuwa arewacin Amerika, Turai da kuma Gabas ta Tsakiya.

:::Yan majalisa zasu bawa yan Nigeria rabin albashin su suboda cire tallafin Fetur

Haka zalika binciken yace kaso 66, na al’ummar Nigeria na rayuwa babu aikin yi, da ake kyautata zaton haka ne yasa mafi yawan mutane ke da burin ficewa don neman aiki a wasu kasashen da suke da cigaba.

Binciken yace a cikin shekaru 2, yan Nigeria miliyan 3,679,496, suka fita daga kasar saboda neman aikin yi.

Haka zalika wani binciken da African Polling Institute, suka fitar a shekarar 2022, ya bayyana cewa kaso 69, na al’ummar Nigeria masu shekaru daga 18-35, suna son barin Kasar in har suka samu dama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here