Manufofin CBN na shekarar 2024 basu yi amfani ba—Majalisa

0
35

Majalisar dattawa ta nemi Gwamnan babban bankin kasa CBN, Olayemi Cardoso, yayi nazari akan manufofin da yake aiwatarwa a fannin kudi, inda majalisar tace mafi yawancin manufofin da akayi amfani da su a 2024 basu amfanar da Nigeria ba.

Kwamitin kula da bankuna da cibiyoyin kuɗi da na inshora na Majalisar ya kuma nemi jin bahasi a kan matsalar ƙarancin takardun kuɗi da ake fama da ita yanzu, da kuma ƙaruwar tsofaffin kuɗi a hannun mutane.

A cikin Wannan shekara mai karewa dai takardar kudi ta Naira ta fuskanci koma bayan da bata taba yi ba, wanda har sai da aka canjar da kowacce Dala daya akan naira 1800.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here