An saki Yahaya Bello daga Gidan gyaran hali na Kuje

0
31

Mahukuntan Gidan gyaran hali na Kuje, sun saki tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello, bayan cika sharudan belin da wata babbar kotun tarayya dake birnin tarayya Abuja ta gindaya masa.

Mai magana da yawun gidan gyaran hali na Abuja, Adamu Duza, ne ya sanar da hakan a yammacin yau juma’a.

A baya kotu ta bayar da umarnin cewa sai Yahaya Bello, ya samu mutane biyu masu gidaje a Abuja sun tsaya masa, tare da bayar da naira miliyan 500.

Idan za’a iya tunawa hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa, ce ta gurfanar da Yahaya Bello, bisa zargin sa da karkatar da naira biliyan 110, na jihar Kogi, a lokacin Mulkin sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here