Gwamnatin tarayya ta yi kasafin naira biliyan 27, a matsayin kudin da za’a biya tsaffin shugabannin Nigeria da mataimakan su hakkin su na shekarar 2025.
Bayan tsaffin shugabannin za kuma a biya tsaffin shugabannin Nigeria na mulkin soji, sai tsaffin shugabannin ma’aikatan fadar shugaban kasa, da tsaffin shugabannin ma’aikatan gwamnatin tarayya, da kuma farfesoshi, duk a cikin naira biliyan 27 din, kamar yadda wani binciken jaridar Punch ya bayyana.
Wadanda zasu ci ribar kudaden sun hadar da Olusegun Obasanjo, Goodluck Jonathan, Buhari, sai tsaffin mataimakan shugaban kasa da suka kunshi Atiku Abubakar, Namadi Sambo, da Yemi Osinbajo.
Sai Kuma tsaffin shugabannin mulkin soji, irin su Yakubu Gowon, Abdussalami Abubakar, Babangida, da tsohon hafsan sojin kasa Commodore Ebitu Ukiwe.