Shugaba Tinubu ya fasa halartar taro saboda mutanen da turmutsutsun yunwa ya kashe

0
44

Shugaban Nigeria Bola Tinubu, ya dakatar da wani shirin zuwa kallon wasan jiragen ruwa da aka shirya gudanarwar a mahaifiyar sa jihar Lagos, sakamakon yadda bayar da tallafin abincin ya zama wata hanyar mutuwar talakawa masu neman tallafi.

Mai magana da yawun Shugaban Bayo Onanuga, ne ya sanar da hakan inda yace Tinubu, ya fasa halartar taron, saboda jajantawa al’umma akan iftila’in mutuwar mutane a wajen karbar tallafin kayan abinci.

A yau ne wani turmutsutsun karɓar tallafin Abincin kirsimeti, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 17 a yanki Okija, dake karamar hukumar Ihiala ta jihar Anambra.

Wani dan siyasa daga jam’iyyar APGA mai suna Chief Ernest Obiejesi, ya shirya bayar da tallafin.

Makamancin hakan ya faru a Abuja, da Oyo, wanda mutane 40, suka mutu a Oyo, Abuja kuma 10, suka mutu a yau asabar.

Ana kyautata zaton cewa yunwa da ake fama da ita a Nigeria itace sanadiyyar mutuwar mutanen, saboda cikowar al’ummar dake neman taimako.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here