Gwamnatin Kano zata dauki matakin shari’a akan masu kin biyan haraji

0
37
Abba Gida-Gida
Abba Gida-Gida

Gwamnatin jihar Kano zata fara gurfanar da masu kin biyan kudin haraji daga sabuwar shekara mai kamawa.

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ne ya bayyana haka a wajen rufe bitar sanin makamar aiki da aka shiryawa kwamishinoni da manyan sakatarorin gwamnatin jihar Kano a garin Kaduna.

Ya yabawa shugaban hukumar tattara kudaden shiga ta jiha Dr. Zaid Abubakar bisa namijin kokarinsa wanda ya kai ga tarawa jihar Kano sama da naira biliyan uku da digo biyar a kowane wata.

In za a iya tunawa, gwamna Abba Kabir Yusuf ya sauya shugabancin hukumar tara kudaden haraji ta jiha da nufin bunkasa kudin harajin da jihar Kano ke tarawa.

Gwamnatin Kano na hasashen tara naira sama da naira biliyan ishirin duk bayan wata uku a shekarar 2025.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here