An rasa sunan sabbin ma’aikatun da Tinubu ya kirkiro a cikin kasafin 2025

0
32

Shugaban Nigeria Tinubu ya ware Naira tiriliyan 2.3 a matsayin kasafin shekarar 2025 ga Ma’aikatar Wasanni da hukumar Cigaban Neja Delta da makamantan ta, wanda tuni shugaban ya sanar da rushe su.

Idan za’a iya tunawa Shugaba Tinubu, ne ya rushe ma’aikatun lokacin daya jagoranci wani zaman majalisar zartarwa ta tarayya a watan Oktoba

Bayan taron ne ministan yada labarai Muhammad Idris, ya bayyana cewa ayyukan Ma’aikatar Wasanni za su koma ƙarƙashin Hukumar Wasanni ta Ƙasa a yayin da ayyukan Ma’aikatar Neja Delta da dangoginta za su koma hannun sabuwar Ma’aikatar Kula da Cigaban Yankuna ta kasa.

Sai dai duk da haka a cikin kasafin na naira triliyan 49.7 da Tinubu ya gabatar an gano cewa kowacce daga cikin ma’aikatun da aka rushe an ware mata kuɗaɗen gudanarwa da na albashin ma’aikata da kuɗaɗen manyan ayyuka.

An ware Naira tiriliyan 2.4 ga rusasshiyar Ma’aikatar Neja Delta da dangoginta Naira tiriliyan 2.205 na albashi da Naira biliyan 24.5 na manyan ayyuka sai Naira biliyan 1.7 na gudanarwa.

Rusasshiyar Ma’aikatar Wasanni kuma an ware mata Naira biliyan 95, da suka haɗa da Naira biliyan 79.9 na manyan ayyuka da Naira biliyan 14 na gudanarwa, sai albashi Naira miliyan 900.

Sai dai m ba a ware komai ba a kasafin na 2025 ga sabuwar Ma’aikatar Kula da Cigaban Yankuna da Hukumar Wasannin, sannan babu sunayensu a kasafin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here