Wani binciken jaridar Daily trust, ya bayyana cewa akalla yan Nigeria 213, ne suka rasa rayukan su cikin shekaru 11 da suka gabata Sakamakon turmutsutsu a gurare daban daban tsakanin 2013 zuwa 2024.
Sai dai mafi yawancin mutanen sun mutu a guraren karbar tallafin kayan abinci, neman aiki da taron addini.
A cikin kwanaki 6 da suka wuce an samu mabanbantan turmutsutsun daya kashe mutane 72, duk sanadiyyar karbar tallafin kayan abinci a jihohin Oyo, Anambra, da birnin tarayya Abuja.
Kananun yara 40 aka bayar da rahoton sun mutu lokacin wani taro a jihar Oyo, sai mutane 22, da suka mutu a turmutsutsun daya afku a Abuja ranar asabar sai 10 a jihar Anambra.
Haka zalika an samu mutuwar mutane 7 a cikin watan Fabrairun wannan shekara lokacin rabon shinkafar da hukumar hana fasa kwauri ta kasa custom ta kama wanda hakan ya faru a jihar Legas, a lokacin an siyar da shinkafar nai nauyin kilogram 25 akan farashin naira dubu 10, don saukakawa mutane kuncin rayuwa.
A dai cikin wannan shekara mutane 7 sun mutu yayin wani turmutsutsun karɓar zakka a jihar Bauchi.
A watan Afrilu ma mutane 30 sun mutu a Sokoto lokacin karbar tallafin kayan abinci da Sanata Aliyu Wamakko, ya gudanar a jihar Sokoto.
Sai kuma dalibai mata biyu da suka rasu a ranar 22 ga watan Maris lokacin taron yaye dalibai a jami’ar Jihar Nassarawa.
A shekarar 2014, kuwa mutane 16 ne suka mutu lokacin da ake kokarin daukar sabbin ma’aikata a hukumar kula da shige da fice ta kasa, a cibiyoyin hukumar dake Abuja Fatakwal, Minna, da Benin.
Sai a shekarar 2013 da mutane 25 suka mutu lokacin wani taron addini a jihar Anambra.
Wadannan sune wasu daga cikin mutuwar da yan Nigeria suka fuskanta sanadiyyar turmutsutsu.